Gwamnatin Najeriya zata tattauna da hukumomin Nijar

Gwamnatin tarayya ta ce za ta tattauna da hukumomin Jamhuriyyar Nijar domin warware rikicin diflomasiyyar da ke wakana tsakanin kasashen biyu. Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, ya ce Nijeriya na son ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yammacin Afrika, ta hanyar amfani da tattaunawa da diflomasiyya. Ya kuma ce gwamnati ta shirya tattaunawa tsakaninta […] Gwamnatin Najeriya zata tattauna da hukumomin Nijar

Gwamnatin Najeriya zata tattauna da hukumomin Nijar

Gwamnatin tarayya ta ce za ta tattauna da hukumomin Jamhuriyyar Nijar domin warware rikicin diflomasiyyar da ke wakana tsakanin kasashen biyu.

Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, ya ce Nijeriya na son ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yammacin Afrika, ta hanyar amfani da tattaunawa da diflomasiyya.

Ya kuma ce gwamnati ta shirya tattaunawa tsakaninta da Nijar bisa ka’idojin kungiyar ECOWAS, saboda Nijeriya na mutunta ikon Nijar da iyakokinta, tare da kira ga gwamnatin Nijar ta shiga tattaunawar domin neman mafita.

Gwamnatin Najeriya zata tattauna da hukumomin Nijar