Nan zuwa 2025 komai zai daidaita – Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya roki ‘yan Najeriya da su kara hakuri da mulkin Bola Ahmed Tinubu, a kuma dan ba shi lokaci. A sakon da ya fitar na taya Kiristoci murnar bikin Kirsimetinsa da sakataren watsa labaransa, Edwin Olofu, ya fitar, Ganduje ya bayyana cewa yan Najeriya za su fara […] Nan zuwa 2025 komai zai daidaita – Ganduje

Nan zuwa 2025 komai zai daidaita – Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya roki ‘yan Najeriya da su kara hakuri da mulkin Bola Ahmed Tinubu, a kuma dan ba shi lokaci.

A sakon da ya fitar na taya Kiristoci murnar bikin Kirsimetinsa da sakataren watsa labaransa, Edwin Olofu, ya fitar, Ganduje ya bayyana cewa yan Najeriya za su fara jin dadin tsare-tsaren da gwamnati ta dauka na farfado da tattalin arziki nan da shekarar 2025, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce, “Yan Najeriya su nuna juriyarsu ga matakan da Shugaban kasa Bola Tinubu ke dauka domin gyara tattalin arziki, duk da cewa sun kawo wasu matsaloli na wucin gadi.

“An riga an fara ganin sakamakon gyare-gyaren da ake yi. Nan da lokacin bikin Kirsimeti na shekara mai zuwa, tattalin arzikin kasar zai gyaru sosai. Haka kuma, a bangaren tsaro, ana samun ci gaba mai kyau domin an rage yawan ayyukan ƴan bindiga.”

Nan zuwa 2025 komai zai daidaita – Ganduje